Lafiya Jari Ce

Informações:

Sinopsis

Shirin Lafiya yana tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jamaa, Sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Talata da yamma.

Episodios

  • Bayani a kan cutar ƙyanda da yadda za a kare yara daga kamuwa

    13/05/2024 Duración: 09min

    A wannan makon shirin zai yi duba kan cutar kyanda ko kuma measles a turance, cutar da galibi akan ga bullarta a irin wannan lokaci da ake fama da matsanancin zafi musamman a yankunan kasashen yammacin Afrika Sahel.  Zuwa karshen watan Fabarairun da ya gabata, fiye da yara 700 suka harbu da cutar kyanda a jihar Borno cikin watan yayinda zuwa yanzu ta kashe kananan yara 42 a jihar Adamawa yayinda wasu fiye da dubu guda suka harbu.Bari mu bude da rahoton wakilinmu Ahmad Alhassan daga jihar Adamawa, jihar da zuwa yanzu tsanantar wannan cuta ta kyanda ta tilasta kulle makarantu.

  • Yadda matasa ke rungumar tsarin yin kaho a zamanance

    06/05/2024 Duración: 10min

    Shirin lafiya jari ce na wannan mako ya mayar da hankali ne kan tsarin yin kaho a zamanance Dannan alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu

  • Karancin ruwa na haddasa tarin cutuka ga al'ummar arewacin Kamaru

    03/05/2024 Duración: 10min

    Shirin Lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda al’ummar yankin arewacin kamaru ke fuskanta matsalar rashin tsaftatacce kuma wadataccen ruwan sha ba, wanda ke haddasa gagarumar matsala ga lafiyar mazauna yankunan, wannan shi ne maudu’in da shirin na wannan mako zai mayar da hankali akai. Tsaftatacce kuma wadataccen ruwan sha na  matsayin ginshikin lafiyar jama’a wanda kuma rashin ke matsayin babbar barazanar bullar tarin cutuka na cikin wajen jikin bil’ada, sai dai samun ruwan sha ko na amfani ga galibin al’ummomin da ke rayuwa a yankin arewacin Kamaru na matukar wahala.A baya-bayan nan al’ummar yankin na ganin bullar cutuka da dama masu alaka da rashin tsaftataccen ruwan sha ko na amfani, yankin da kashi 43.5 na al’ummarsa ne kadai musamman mazauna karkara kan iya samun wadatacce kuma tsaftataccen ruwa.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shiri.

  • Amfanin Azumi ga lafiyar jikin dan Adam

    01/04/2024 Duración: 09min

    Shirin Lafiya Jari ce a wannan karo ya mayar da hankali ne game da alfanun Azumi ga lafiyar jikin dan Adam. Masana kiwon lafiyar dai na bayyana cewar Azumi na taimakawa wajen rage kaifin wasu cutuka a jikin dan adam. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....

  • Yadda ya kamata mai Azumi ya kula da kansa a lokacin zafi

    25/03/2024 Duración: 09min

    Shirin Lafiya Jari ce a wannan karo ya mayar da hankali ne kan irin cutukan da ke karuwa a lokutan Azumi musamman yadda a wannan karon ake gudanar da ibadar a cikin yanayi na tsananin zafi, wanda masana ke ganin akwai wasu naukan cutukan da ka iya bijorowa. Masana kiwon lafiya dai sun gargadi masu dauke da wasu nau'ukan cutuka kan irin matakan da ya kamata su dauka don kula da lafiyarsu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....

  • Yadda aka yi wa sama da yara dubu dari 9 rigakafin cutar Polio a Kamaru

    18/03/2024 Duración: 10min

    Shirin Lafiya Jari ce a wannan karo ya mayar da hankali ne kan yadda aka gudanar da gangamin rigakafin cutar shan inna wato Polio a Jamhuriyar Kamaru don dakile bazuwarta. A baya-bayan nan ne dai ake ganin bullatar cutar a wasu sassan kasar, lamarin da ya sanya mahukunta tashi tsaye don yin rigakafin cutar. Sama da yara dubu dari 9 da 48 ne aka yi wa rigakafin a fadin jahohi 10 na Kamaru, a aikin da aka kwashe tsawon kwanaki uku ana yi.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....

  • Yadda maza a Najeriya ba sa bai wa gwajin sankarar mafitsara mahimmanci

    04/03/2024 Duración: 10min

    A wannan mako shirin ya mayar da hankali kan nau’ikan cutakan da ba a fiya mayar da hankali wajen yakarsu ba musamman a kasashe masu tasowa irin Najeriya, wannan nau’in cutuka kuwa sun kunshi kansar mafitsara ko kuma Prostate Cancer, nau’in kansar da ke matsayin mafi hadari ga maza, amma kuma ba ta samun kula duk da yadda ta ke kisan akalla mutum dubu 8 duk shekara a Najeriya. 

  • Yadda ake samun karuwar masu kamu wa da cutar cizon mahaukacin kare a Najeriya

    26/02/2024 Duración: 09min

    Shirin Lafiya Jari ce a wannan karo ya mayar da hankali ne kan cutar cizon mahaukacin kare ko kuma Rabies a turance, bayan da bincike ya nuna cewar cutar na karuwa a Najeriya duk da cewa babu cikakkun alkaluman wadanda cutar ta shafa saboda karancin kawo rahoton cutar ga mahukunta. Sai dai wasu alkaluman hukumar dakile yaduwar cutuka ta Najeriyar NDDC sun nuna cewa daga shekarar 2017 zuwa 2022 akwai akalla mutane 998 da kuma karnuka 273 da suka harbu da cutar ta Rabies ko kuma cizon mahaukacin kare.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....

  • Cutar kazuwa ta addabi al'ummar wasu yankunan Jamhuriyar Nijar

    19/02/2024 Duración: 09min

    A wannan makon shirin Lafiya Jari ce ya mayar da hankali ne kan cutar kazuwa ko kuma Smallpox a turance, cutar da ke sahun cutuka masu matukar hadari da ke haddasa kuraje masu matukar kaikayi da mashasshara da kuma hana barci, wadda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta sanar da kawar da ita daga ban kasa tun a shekarar 1980 amma kuma duk da haka ake ganin bullarta lokaci zuwa lokaci. Cutar ta kazuwa wadda ake alakantawa da kazanta a baya-bayan nan ne aka samu barkewarta a wasu kauyukan Jihar Maradi ta Jamhuriyyar Nijar, inda masana ke cewa zuwa yanzu akwai fiye da mutum dubu 3 da suka harbu, kuma kaso mai yawa na Almajirai da magidanta sai kuma kananan yara musamman a kauyukan Surori zuwa Tsibiri da kuma garin Udal, wanda ke matsayin karon farko da aka ga bullar cutar bayan shafe tsawon shekaru ba tare da jin duriyarta ba.Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Azima Bashir Aminu....

  • Yawaitar gurbatattun jami'an lafiya a asibitocin Najeriya

    29/01/2024 Duración: 10min

    A wannan makon shirin ya mayar da hankali kan yawaitar gurbatattun jami’an lafiya a asibitocin Najeriya wanda ke da nasaba da kodai rashin samun cikakken horo a kwalejojin lafiya ko kuma samun horon irin wadannan makarantu amma na bogi.A baya-bayan nan ana yawan ganin yadda ake bude tarin makarantu masu zaman kansu a sassan Najeriya da sunan horar da jami’an lafiya kama daga kwalejoji har da jami’o’I wadanda wasu daga cikinsu kan rasa sahalewar mahukuntan saboda rashin cancanta.

  • Yadda saran maciji ke haddasa asarar dimbin rayuka duk shekara a Najeriya

    22/01/2024 Duración: 10min

    Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya yi duba ne kan illar dafin miciji ga lafiyar bil'adama dai dai lokacin da asibiti daya tilo da ke lura da wadanda suka gamu da cizon na maciji ke ganin koma baya. Asibitin wanda ke jihar Gombe a Najeriya yanzu haka na fuskantar kalubale rashin tafiyarwa ta yadda baya iya bayar da gudunmawa kamar yadda ya dace ga dimbin majinyatan da ke ziyartarshi bayan haduwa da cizon maciji.Baya ga rashin wuta da rashin isassun jami'an kula da marasa lafiya, matsalar tsadar magunguna a asibitin na matsayin dalilin da ke hana mutane zuwa duba lafiyarsu ko da sun hadu da ibtila'in na cizon maciji.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...........

  • Najeriya ta fara amfani da fasahar tiyata ba tare da tsaga jiki ba

    18/12/2023 Duración: 09min

    A wannan mako shirin ya mayar da hankali ne kan ci gaban da aka samu na fara amfani da fasahar fida ba tare da tsaga jikin majinyaci ba a Najeriya, a wani yunkuri na rage dogaro da kasashen ketare wajen irin wannan fida.   Wannan ci gaba dai ya biyo bayan koken kungiyar likitocin sashen gwaje-gwajen cutuka ta Najeriya wadda a yayin taronta na 206 ta bayyana cewa lokaci yayi da ya kamata a ce Najeriya ta zama kasar da za a rika tururuwa don shigowa neman magani idan har da gwamnatoci sun yi abin da ya dace.   kuma dangane da haka ne asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke garin Bauchi, ya kaddamar da wata na’urar fede marar lafiya ba tare da tsaga jikinsa ba, kamar yadda shugaban asibitin Dr Yusuf Jibril Bara ke cewa.

  • Najeriya za ta maida tsoffin likitoci bakin aiki domin cike gibin jami'an lafiya

    13/11/2023 Duración: 09min

    Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wanna makon tare da Murtala Adamu Ibarhim ya maida hankali ne kan shirin gwamnatin Najeriya na sake daukar likitoci da sauran jami'an kiwon lafiya wadanda suka yi ritaya daga aiki, a wani kokari na cike gibin karancin jami'an kiwon lafiya a kasar, masamman guraben wadanda suka tsere zuwa kasashen waje domin samun albashi mai soka.

  • Yadda ake gano cutar koda da kuma hanyar magacen ta ( Kashi na 2)

    26/10/2023 Duración: 09min

    Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon ya tattauna ne kan musabbabin kamuwa da ciwon koda a daidai lokacin da wasu alkaluma ke nuni da cewa, akwai mutane kimanin miliyan 17 da ke fama da cutar a Najeriya. Shirin ya kuma yi dubi kan kalubalen da masu fama da cutar ke fuskanta musamman dangane da samun kudin kwanke kodar a Najeriya ko kuma kudin sayen maganin cutar.Shirin ya tattaunawa da kwararrun likitoci wadanda suka yi cikakken bayani kan yadda wannan cuta ke kama jama'a da kuma yadda za a kauce mata.Kazalika shirin ya zanta da masu fama da cutar ta koda, inda suka yi bayani kan yadda suke ji a jikinsu da kuma hanyar da suke bi wajen kokarin magance ta.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu

  • Yadda ake gano cutar koda da kuma hanyar magacen ta ( Kashi na 1)

    26/10/2023 Duración: 09min

    Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon ya tattauna ne kan musabbabin kamuwa da ciwon koda a daidai lokacin da wasu alkaluma ke nuni da cewa, akwai matasa kimanin miliyan 5 da ke fama da ciwon koda a kasar Ghana. Shirin ya tattaunawa da kwararrun likitoci wadanda suka yi cikakken bayani kan yadda wannan cuta ke kama jama'a da kuma yadda za a kauce mata.Kazalika shirin ya zanta da masu fama da cutar taa koda, inda suka yi bayani kan yadda suke ji a jikinsu da kuma hanyar da suke bi wajen kokarin magance ta.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu

  • Mutane dubu 131 suka kamu da cutar Kansa a bara a Najeriya

    09/10/2023 Duración: 10min

    Shirin a wannan mako ya yi duba kan karuwar masu kamuwa da cutar kansa ko kuma Sankara koma Daji kamar yadda hausawa ke kira, cutar da a bara kadai Najeriya ta samu sabbin kamuwa akalla dubu 131 baya ga wasu dubu 78 da cutar ta kashe. 

  • Ciwon idanu na Apollo ya sake bayyana a sassan Najeriya

    02/10/2023 Duración: 10min

    Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon ya tattauna da masana akan matsalar ciwon idanu na Apollo da a baya bayan nan ya sake bulla a sassan Najeriya. Cikin shirin za a ji dallilan da suka janyo sake bayyana ciwon idanun da kuma matakan da za a dauka wajen magance shi ko kuma dakile yaduwarsa.

  • Yadda hanyoyin gargajiya ke samun karbuwa wajen magance cutar sikila

    18/09/2023 Duración: 10min

    Shirin 'Lafiya Jari Ce'  na wannan mako ya yi nazari ne kan hanyoyin gargajiya da ake bi wajen magance cutar  sikila  da kuma yadda al'umma suka karbi wadannan hanyoyi don samar wa kansu mafita. Shirin ya tattauna da masu maganin gargajiya da ke ikirarin cewa magungunansu na samar da waraka, kana ya gana da  liitocin zamani don neman karin haske a kan inda aka kwana wajen neman mafita a game da wannan cuta ta sikila. 

  • Yadda Fasahar dashen ciki ke kara samun karbuwa a Najeriya

    11/09/2023 Duración: 09min

    Shirin Lafiya Jari na wannan mako ya duba irin nasarorin da ake samu ta fannin yiwa matan da suka kasa daukar ciki dashen cikin a kimiyyance. Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Azima Bashir

  • Kalubalen da mata ke fuskanta a yayin haihuwa

    04/09/2023 Duración: 10min

    Shirin lafiya jarice na wannan mako, ya duba irin kalubalen da mata ke fuskanta a yayin daukar ciki, haihuwa da kuma rainon jarirai.

página 1 de 2